DSS Ta Musanta Batun Daƙume Alƙalin Kotun Shari’ar Zaɓen Kano
Rundunar ƴan sandan farin kaya (DSS), ta musanta rahoton da ke bayyana cewar, Jami’anta sun daƙume guda daga cikin Alƙalan Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan Kano.
Wannan musantawa da hukumar ta yi kuma, na zuwa ne bayan kalamin da Sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi, wanda ya ce Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewar hukumar tsaro ta farin kaya ta daƙume Alƙalan da su ka yanke hukunci kan shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano.
Sai dai, a ya yin da ya ke zantawa da Jaridar PRNigeria, ta wayar tarho, Kakakin rundunar ta DSS, Dr. Peter Afunanya, ya musanta iƙirarin, Mai magana da yawun Gwamnan na Kano.
Ya na mai cewar, ” Wannan rahoto ba gaskiya bane. To mu kama Alƙalai ma, saboda wanne dalili ?, Ba gaskiya bane”.
Tun da fari dai, a ya yin zantawarsa da kafar Talabijin ta Channels, Sanusi Bature ya ce, “Babu dalilin da zai sa DSS su tsare Alƙali, ba tare da ya aikata komai ba. Tsare guda daga cikin Alƙalan da su ka yanke hukuncin shari’ar zaɓen Gwamnan Kano, da DSS ta yi, zalinci ne, da tauye ƴanci”.
“Ko yanke hukuncin da su ka yi, ta hanyar intanet ma, bamu san daga ina su ka yanke hukuncin ba. Sun dai yanke hukuncin ne, a wani killataccen wuri, ko makamancin haka. Ba mu san a inda su ke ba, kuma bamu san wanne hali su ke ciki ba, saboda mu kawai muna kallonsu a majigi ne.
“Abubuwa da dama sun faru a bayan fage, babban abin da ya bamu mamaki ma, shi ne wanda aka bayyana a matsayin mai nasarar, ba ya cikin waɗanda su ka shigar da ƙara. Gawuna ya tsaya zaɓe, ya kuma karɓi ƙaddarar faɗuwar da ya gamu da ita, tare da taya, Abba Kabir murna, ya ma ce ba zai je Kotu ba”.