Tsaro

Dubun Wasu Sojojin Bogi Ta Cika

Rukunin 81, na rundunar Sojin ƙasar nan, sun samu nasarar cika hannunsu da wasu Jami’an bogi guda shida.

Laftanal Ayodeji Owoyomi, wanda ya yi bayani a madadin Kwamandan rukunin rundunar ta 81, Birgidiya Janar Mohammed Abubakar, shi ne ya bayyana hakan, ranar Litinin, ya yin da ya ke zantawa da manema labarai, a ofishin rundunar, da ke Victoria Island, a jihar Lagos.

Wasu daga cikin Jami’an bogin da aka kama ɗin dai, na sanye ne da Kayan Sojoji, inda ake zarginsu da haɗa dandazon ababen hawa.

Da ya ke holin masu laifin, Owoyomi, ya ce abubuwan da Jami’an bogin su ka aikata abu ne da ya kawo gagarumar matsala, inda kuma tuni aka daƙume Jami’an, tare da damƙasu a hannun Jami’an ƴan sanda.

A wasu lokutan ana ganin yawaitar aikata irin waɗannan abubuwa na sojin gona, ba ya rasa nasaba da kaunar aikin, Ya yin da a wani ɓangare kuwa, hakan ke kasancewa hanyar cutar da al’umma.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button