Dukkan Ɗaliban Da Takardun Karatun Su Basu Da Inganci, Ba Za Su Yi Hidimar Ƙasa Ba – NYSC
Darakta Janar, na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya jaddada cewar, dukkannin ɗalibin da bai cika sharuɗɗan da ake buƙata kafin zuwa hidimar ƙasa, na tsawon shekara guda ba, ba zai samu sahalewar zuwa hidimar ƙasar ba.
Ta cikin wani jawabi, da aka fitar, jiya (Alhamis), a babban birnin tarayya Abuja, ɗauke da sa hannun Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Eddy Megwa, hukumar tace wasu daga cikin Makarantu da Jami’o’in nahiyar Afirka, su na yaye ɗaliban da basu cancanta ba, hakan ne ya sanya hukumar ta fito da wani shiri mai taken, “Daƙile ƙalubalen da ake fuskanta, daga Ɗaliban da su ka kammala Digiri a ƙasashen ƙetare, Domin hidimtawa ƙasa yadda ya dace”.
Ya kuma jaddada cewar, an samar da shirin hidimtawa ƙasa ne, da nufin sake haɗa kan matasan Najeriya, ta hanyar yaɗuwar kyawawan ɗabi’u irinsu jajircewa, gaskiya, riƙon Amana, da ma dogaro da kai.
Sai dai, ya koka kan yadda manyan makarantu da mamallaka makarantun ke yunƙurin sauya wannan manufa zuwa hanyar samun kuɗi wanda ke kaiwa ga yaye ɗaliban da basu cancanta ba.
“Muna sa ran daga rukunin A na shekarar 2024, wajibi ne mudinga karɓar jerin sunayen ɗaliban da su ka kammala makarantu, a ƙasashen Jamhuriyyar Nijar, Kamaru, Ghana, da Uganda, waɗanda su ne su ke samar da kaso 20 na Ɗaliban da ke kammala makarantu a nahiyar Afirka, domin tantancewa.
Za mu bunƙasa wannan shiri zuwa ga ɗaukacin ƙasashen da aka fi yawan samun jabun takardun Makaranta, da na tafiye-tafiye”, a cewarsa.
Ya kuma ce, daman tuni akwai wannan tsarin a makarantun Najeriya, tun tsawon lokaci, kuma an ga alfanun da ya ke samarwa.