EFCC Ta Gurfanar Da Ɗaliban Jami’a 11 A Gaban Kotu
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC, shiyyar Ibadan, ta bayyana cewar, ta gurfanar da Ɗaliban Jamiár Obafemi Awolowo, da ke Ile-Ife, guda 11, a gaban Mai Sharia Nathaniel Ayo-Emmanuel, na Babbar Kotun Tarayya, da ke Osogbo, a jiya, bisa zarginsu da damfarar jamaá ta yanar gizo.
An gurfanar da ɗaliban ne bisa tuhume-tuhume mabanbanta, waɗanda su ka fara daga laifi guda ɗaya zuwa shida.
Ta cikin wani jawabi da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jamaá na hukumar, Dele Oyewale, ya fitar, a Ibadan ya bayyana cewar, waɗanda ake zargin sun haɗarda: Perekebena Micah, Nnekwelugo Nnaemeka, Moyosore Oluwasakin, Aghwaritoma Obaro, Daniel Maiye, Gbolahan Adesina, Yinka Jayeola, Olumuyiwa Adeleye, Abiola Oluwadare, Busari Ayodeji, da Okesipe Paul.
Tara daga cikin ɗaliban da aka gurfanar ɗin kuma, ana zarginsu ne da aikata laifuka ɗai-ɗai, ya yin da ragowar biyun kuwa, ake zargin Micah da laifuka biyu; sai Obaro da aka gurfanar da shi bisa zargin aikata laifuka shida.