EFCC Ta Kama Motoci 25 Maƙare Da Ma’adanan Ƙasa
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zakon kasa ta EFCC, reshen Ilorin, ta bayyana yadda ta kama wasu manyan motoci guda 12, makare da maádanan kasa samfurin Solid Minerals, wadanda take zargin an hako su ne, a jihar Kwara, ba tare da samun lisisi ba.
Da ya ke holen wadanda ake zargin, ranar Talata a birnin Ilorin, Kwamandan rundunar ta EFFC, Michael Nzekwe, ya bayyana cewar an kama mutanen ne, a wurare daban-daban, da su ka hadarda Patigi, Igbeti, da Ogbomoso, da ke kusa da jihar ta Kwara.
Ya kuma ce, daurin rai-da-rai ne hukuncin dukkannin wadanda aka samu da aikata irin wannan laifi, kamar yadda sashe na 1(8)(b) na dokar laifuka ta Miscellaneous Offences Act, Cap M17, ta shekarar 1983 ta yi tanadi.
A karshe, ya yi gargadin cewa, hukumar ta EFCC ta za ta saurara kan manufar da aka samar da ita ta yaki da cin hanci da rashawa ba, dan haka ba zata zuba id tana ganin ana gudanar da ayyukan da basu dace ba, a haramtattun cibiyoyin hakar maádanan kasar, da ke fadin kasar nan.