Zamantakewa
EFCC Ta Yi Gargaɗi Kan Saƙon Bogi
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), ta gargadi al’ummar ƙasar nan game da saƙonnin bogin da ake tura wa jama’a, da sunan ofishin bayar da Agaji na hukumar.
Hukumar dai, a jiya Talata ta cikin wata sanarwa da ta fitar, mai taken ‘A lura da saƙonnin ƙarya’ ta ce babu wani makamancin ofishin da ke da wannan suna, a hukumar.
Gargadin da hukumar ta fitar kuma, na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar , Wilson Uwujaren ya sanyawa hannu.
A ƙarshe hukumar ta shawarci al’umma da su kula matuƙa, tare da ƙoƙarin tantace duk wani saƙo da aka tura musu, musamman waɗanda ke da alaƙa da neman bayanan su.