Ƙasashen Ƙetare

Egypt Ta Buɗe Iyakarta Domin Kwaso Ɗaliban Najeriya

An buɗe iyakar ƙasar Misra (Egypt), domin aikin kwaso Ɗaliban Najeriya, da su ke cigaba da maƙalewa a ƙasar Sudan.

Bayanin hakan ya fito ne, ta cikin wani saƙo da hukumar kula da al’ummar ƙasar nan da ke zaune a ƙasashen ƙetare ta wallafa, ranar Litinin, a shafinta na kafar sadarwar Twitter.

Inda hukumar ta ce, ”Halin Da Ake Ciki : Bisa sahalewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ƙarshe dai ƙasar Egypt ta buɗe Iyakarta, domin kwaso al’ummar Najeriya, da ke maƙale, a Sudan. Tuni kuma Jirgin Sojojin sama ya sauka a Aswan, da ke Egypt, inda ya ke shirin fara kwaso rukunin farko na jama’ar da zai dawo da su ƙasar nan.

Najeriya na yunƙurin kwaso jama’arta daga ƙasar ta Sudan ne dai, ya yin da ake cigaba da fuskantar musayen wuta tsakanin rundunar sojin ƙasar, da dakarun RSF.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button