Elon Musk Ya Maka OpenAI A Kotu, Bisa Zargin ‘Butulci’
Fitaccen masanin fasahar nan na duniya, Elon Musk, ya maka kamfanin OpenAI a gaban Kotu, wanda shi ne AI ɗin da ya tallafa wajen tabbatar da kafuwarsa shekarar 2015, ya na zargin shuwagabanninsa da ‘butulcewa’ ainihin manufa da shirinsu.
Musk, ya zargi kamfanin Microsoft, da sarrafa OpenAI ɗin a lokuta da dama, duk kuwa da musanta iƙirarin da kamfanonin ke cigaba da yi.
Tuni kuma AFP ta tuntuɓi dukkannin kamfanonin, domin jin ta bakinsu game da ƙarar da aka shigar.
Shigar da ƙarar kuma, ya ja hankalin duniya, sakamakon kasancewarsa tsakanin manyan kamfanonin Fasaha na duniya, da ke tsaka da tashe.
Tuni kuma ɗai-ɗaikun jama’a, da kamfanoni da dama su ka sanya ido, dan ganin yadda za ta kasance.
Kuma ku cigaba da kasancewa da Jaridar Rariya Online, domin cigaba da sanin halin da ake ciki, da ma ƙarin wasu labaran na duniya.