Kasuwanci

Equatorial Guinea Ta Haɗa Hannu Da Kamfanin Shinkafar Tiamin Dan Bunƙasa Noma A Afirka

Ƙasar Equatorial Guinea ta haɗa guiwa da babban kamfanin samar da shinkafa a ƙasar nan na Tiamin Rice, domin bunƙasa harkokin noma, da samar da tsaro ta fuskar abinci, a ɗaukacin nahiyar Afirka.

Jakadan ƙasar ta Equatorial a ƙasar nan, Francisco Mague, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani jawabi da Jamiín lura Alámuran Kasuwanci na kamfanin, Mohammed Inuwa Danja ya fitar, a babban birnin tarayya, Abuja.

A ya yin da ya kai ziyara kamfanin na shinkafar Tiamin da ke jihar Bauchi, Mague, ya yabawa kamfanin bisa yadda su ke amfani da kayayyakin fasahar zamani wajen bunƙasa samfurin shinkafar da su ke fitarwa.

Inda ya ce ire-iren kayayyakin, abubuwa ne da ke sauƙaƙa ayyuka, tare da sanya kamfanin taka muhimmiyar rawa wajen samar da wadatattun kayayyakin abinci, a kasuwanninsu.

Mague, ya kuma ce, haɗa guiwar da su ka yi, zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa wanzuwar wadataccen abinci a nahiyar Afirka, da ma bunƙasa tsaro ta fuskar tattalin arziƙi da isashshen abinci a yankin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button