Labarai

Fankon Kundin Kasafin Kuɗi Tinubu Ya Gabatar Mana – Majalissar Wakilai

Wani Ɗan Malissar tarayya mai suna, Hon. Shitu Galambi, daga jihar Jigawa, ya bayyana cewar, fankon kasafin kuɗi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatarwa Majalissar, a ranar Larabar da ta gabata.

Ɗan Majalissar ya ce, abinda Bola Tinubun ya gabatarwa gamayyar zauren majalissun bai wuce bayanin baki ba kawai, domin kundin da ya direwa Majalissun bai ƙunshi kasafin kuɗin da aka warewa kowacce ma’aikata ba.

Hon. Galambi, ya bayyana hakan ne, ranar Juma’a, a ya yin zantawarsa da sashen Hausa na BBC.

Idan ba a manta ba dai, a ranar Larabar makon da mu ke bankwana da shi ne, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a gaban haɗakar zaurukan Majalissun ƙasar nan.

An kuma kira kasafin kuɗin na kimanin Naira tiriliyan 27.5 da sunan ‘Kasafin sake farfaɗo da fata’, wato ‘Budget For Renewed Hope’ a harshen Ingilishi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button