Fargaba Ta Mamaye Jama’a Bayan Hukuncin Kotun Zaɓe, A Kano
Tsoro da fargaba sun mamaye zuciyoyin al’ummar jihar Kano, biyo bayan hukuncin da Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar ta zartar, wanda ya sutale Gwamna Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP, daga kan kujerarsa, tare da miƙa nasara ga Nasiru Yusuf Gawuna, na jam’iyyar APC.
Tuni kuma Ƴan Kasuwa da dama su ka fara rufe shagunansu, a kasuwanni daban-daban na jihar ta Kano, inda su ke haba-haba wajen garzayawa gida.
Rahotanni daga wasu unguwannin cikin birni kuwa, na bayyana yadda aka fara samun tashe-tashen hankula, tare da fito da makamai, ya yin da rundunar ƴan sanda ke cigaba da kama waɗanda aka samu ɗauke da Makaman.
Kotun sauraron ƙarar zaɓen dai, ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta soke takardar lashe zaɓen da ta damƙawa Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP, tare da bada takardar shaida ga Nasiru Yusuf Gawuna, na APC.
Wannan hukunci kuma, ya biyo bayan soke ƙuri’u kimanin 165,633 da Kotun ta yi ne, bisa hujjar rashin samun sitamfi da kwanan wata a jikinsu.