Kimiyya Da Fasaha

Fasahar AI Za Ta Iya Raba Kowanne Mutum Da Aikinsa – Elon Musk

Fitaccen jagoran al-amuran fiƙirar nan, mamallakin kamfonin Tesla, SpaceX, da X (wacce aka fi sani da Twitter a baya), da kuma sabon kamfanin fasahar AI mai suna xAI, Elon Musk, ya ce fasahar na’ura mai fikira irinta Ɗan Adam (Artificial Intelligence) za ta iya raba kowanne Mutum da aikinsa.

Musk ya ce, kaitsaye ba za a iya iyakance yadda fikirar za ta bunƙasa a matakin ƙololuwa ba, kawai dai abin da ya sani shi ne, za a kai matakin da na’urorin na AI za su iya aiwatar da komai da mutum ya ke buƙata a rayuwa, dan haka a irin wannan gaɓar ba a buƙatar wani Ma’aikaci.

Musk, ya kuma bayyana hakan ne, ya yin da ya halarci wani taro da aka gudanar, a gidan Gwamnatin Burtaniya (Lancaster House).

Inda a ya yin da ya bayyana a gaban Fira Ministan Burtaniya, Rishi Sunak, ya cigaba da cewa, “Za ka iya samun aiki, idan kanason za ma mai aikin yi domin samarwa kanka gamsuwa. Amma babu shakka AI zai iya yin komai.

“Bansani ba, ko hakan zai sa mutane su samu nutsuwa ko akasin haka”., Musk ya faɗa cikin raha, ya yin da mahalarta taron su ka tuntsure da dariya.

Ka zalika ya bayyana cewar, ire-iren ayyukan Ɗan Adam da saƙagon na AI ke gudanarwa, abu da zai sanya ya zama mai haɗari fiye da makamin Nuclear.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button