Labarai

FBI Ta Daƙume Sabon Shugaban Ƙaramar Hukuma, Kan Zargin Zamba

Hukumar bincike ta FBI, ta cika hannu da sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukumar, Ogbaru, da ke Jihar Anambra, bisa zargin aikata zambar sama da Dalar Amurka Miliyan 3.3.

FBI, ta daƙume Shugaban Ƙaramar Hukumar mai suna, Nwadialo ne, a ranar Juma’a, gabanin isarsa birnin Texas, na ƙasar Amurka.

Hukumar ta FBI dai, na zargin Shugaban Ƙaramar Hukumar, ta Ogbaru, da ke Kudu Ta Tsakiyar Najeriya ne, da zama ƙusa a wata tawagar ƙasa da ƙasa da ke zambatar al’umma cikin aminci (ta hanyar yanar gizo).

Har ya zuwa yanzu kuma, babu wani tartibin bayani daga ƙaramar hukumar ta Ogbaru, game da lamarin, duk da cewa labarin na cigaba da yamutsa hazo a duniyar Siyasa da Tattalin Arziƙi.

Ana sa ran, hukumar ta FBI za ta fitar da sanarwa, kan halin da bincikenta yake ciki, kowanne lokaci daga yanzu, yayin da su ma Lauyoyin Nwadialo ɗin su ka gaza cewa ‘uffan’ kan lamarin.

Hukumomi daban-daban daga ƙasar Amurka, da Najeriya ne kuma ke cigaba da sanya ido kan binciken.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button