Fitacciyar Ƴar Wasan Kokawa, Blessing Oborududu Ta Je Wasan Daf Da Na Kusa Da Na Ƙarshe
Zakarar ƴar gasar ƙasashen rainon Burtaniya na Commonwealth, har karo biyu, wacce kuma ta lashe kyautar silva a gasar, Blessing Oborududu, ta na fatan samun tikitin halartar wasannin Olympic na shekarar 2024, da za a gudanar a ƙasar Paris, ya yin da za ta gudanar da wasan neman cancanta a Belgrade, na ƙasar Serbia, a yau Laraba.
Takwararta, Odunayo Adekuoroye, wacce ta samu rashin nasara a wasan dab da na kusa da na ƙarshe da ya gudana a ranar Talata, za a duba yiwuwar karramata da kyautar zoben tagulla, wanda zai nuna ƙwazonta daga cikin jerin zakarun ƴan wasan Olympic, da za ta gudana a ƙasar Paris, a shekara mai kamawa.
Ƴar wasan ta fara fafata wasanninta ne da ƙwarin gwuiwa, inda ta samu nasara da maki 9 da 7, akan ƴar wasan duniya ta 4, Guilla Olivera, a zagaye na 16, bayan da ta ɗaga ƴar wasan ta Brazil ta makata da ƙasa, a gasar kokawa ta masu nauyin gram dubu 57.
Daga nan ne kuma, sai tsohuwar lamba ɗayan duniya da ke ƙasar India, Sarita Mor, da cire ƴar wasan ta Najeriya Adekuoye mai matsayi na 22 a gasar, da maki 6 da 4, a wasan daf da na kusa da na ƙarshe.
A yanzu kuma, ƴar wasan mai shekaru 29 a duniya, za ta fafata da Repechage, a yau Laraba, domin neman samun damar zuwa wasan ƙarshe.