Labarai

Fursunoni 300 Ne Ke Tsare A Gidan Yarin Kano, Ba Tare Da Aikata Laifin Komai Ba

Kwamitin bincike da bada shawara, wanda Babban Sufeton rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Kayode Egbetokun ya kafa, ya gano yadda ake tsare da fursunoni 300 a gidan gyaran hali na Kurmawa, da ke birnin Kano, ba tare da sahihan takardun da ke bayyana abinda ake tuhumarsu da aikatawa ba.

Kwamitin, ya bayyana abin da ya zaƙulo ne, ranar Laraba, a cigaba da ziyarar da ya ke kaiwa Cibiyoyin Gyaran Halin da ke faɗin ƙasar nan.

Ziyarar da kwamitin ya kai gidan gyaran halin na Kurmawa kuma, an kaita ne, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, CP Muhammad Hussaini Gumel.

Da ya ke zantawa da manema Labarai, bayan ziyarar, Gumel ya ce maƙasudin kai ziyarar shi ne domin gano ire-iren waɗannan matsaloli, da kuma tattara su, tare da aike su ga hukumomin da lamarin ya shafa, domin ɗaukar matakan da su ka dace.

Wasu daga cikin fursunonin da ke cikin wannan lamari dai, basu san ma kotun da take da alhakin sauraron shari’unsu ba, wasu kuwa ana tsare da su ne tsawon shekaru ba tare da gabatar da takardun abinda ake tuhumarsu da shi ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button