Kotu

Garƙame Layukan Da Ba a Haɗa Da Lambobin NIN Ba, Ya Jawo Maka Kamfanonin Sadarwa A Kotu

A yau (Litinin) ne, wani mutum mai fafutukar kare haƙƙoƙin ƴan Adam, Mr Olukoya Ogungbe, ya shigar da ƙarar kamfanonin sadarwa na Najeriya a gaban Babbar Kotun Lagos, ya na ƙalubalantar matakin da su ka ɗauka na toshe layukan wayoyin ƴan ƙasa.

Waɗanda mai ƙarar ya shigar a matsayin waɗanda ya ke ƙara dai, su ne: Hukumar Sadarwa Ta Ƙasa (NCC), Dr. Aminu Mada (Shugaban NCC), da Kamfanin Sadarwa na MTN Nigeria Communications Plc.

Sauran su ne: Airtel Networks Nigeria Ltd. Globacom Ltd da Emerging Markets Telecommunication Services Ltd. (EMTS 9 Mobile).

A cikin ƙunshin ƙarar tasa, Ogungbe ya ce tun a watan Janairun shekarar da mu ke ciki, waɗanda ya ke ƙarar sun yi barazanar toshe dukkannin layukan da ba a haɗa su da lambobin ɗan ƙasa na NIN ba.

Hakan kuma ya sanya ya garzaya Kotu, tare da karɓo umarninta (Court Order) a ranar 22 ga watan Fabrairun da ya gabata, wacce ke dakatar da kamfanonin daga aikata abin da su ka ƙudirta na rufe layukan ƴan Najeriya, har sai an saurari ƙarar da ya shigar.

Amma ga mamakinsa, a ranar 28 ga watan na Fabrairun da ya gabata, kawai sai ya ga an rufe layukan mutanen Najeriyar, wanda hakan ke nuni da bijirewa tare da raina umarnin Kotu kaitsaye.

A yanzu kuma, mai ƙarar ya na buƙatar Kotun ne ta ayyana toshe layukan da kamfanonin su ka yi, a ranar 28 ga watan Fabrairu, a matsayin haramtacce, duba da yadda aka aiwatar da shi ta hanyar bijirewa umarnin Kotu.

Ka zalika, Ogungbe ya buƙaci Kotun da ta tilastawa waɗanda ya ke ƙarar buɗe layukan wayoyin da su ka toshe.

Bugu da ƙari, ya buƙaci Kotun da taci tarar kamfanonin Naira biliyan 10, sakamakon asarar da su ka jawowa al’umma sanadiyyar toshe layukan ƴan Najeriyar.

Baya ga haka, ya buƙaci Kotun da ta dakatar da kamfanonin layukan daga ɗaukar kowanne irin mataki na gaba, muddin zai iya shafar ƴan ƙasa.

Zuwa yanzu kuma, ba a sanya wata rana domin fara sauraron shari’ar ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button