Gidauniyar AMG Za Ta Gina Banɗakai Samfurin ‘Triple 10’ A Kano
Biyo bayan kammala aikin ginin bandakai da Gidauniyar Aminu Magashi ta kaddamar a Geza, da ke karamar hukumar kumbotso, Gidauniyar ta kuma ce za ta kaddamar da wani aikin ginin bandakan na daban da zai lakume sama da Naira miliyan 3, wajen aikin gina makewayai masu ciki uku-uku guda goma, da gidauniyar ta kira da “Triple 10”.
Daraktan Ayyuka na gidauniyar, Malam Suleiman Jalo ne ya bayyana hakan, yayin taron masu ruwa da tsaki na kungiyar matasa masu yunkurin dakile cuttutuka masu yaduwa ta YOSPIS, tare da gamayyar tabbatar da samuwar Ilimi ga kowa da kowa CSACEFA a takaice.
Jalo kara da cewar, za a kaddamar da karin wasu ayyukan na Triple 10, na YOSPIS da CSACEFA, a makarantun Firamare 10, na jihar Kano, inda za su lakume Naira miliyan uku da dubu dari biyar.
Za kuma a zakulo makarantu goman da za su amfana da tsarin ginin bandakan na Triple 10, ta hanyar duba tsantsar bukatar makarantun.
Gidauniyar ta AMG, YOSPIS, da CSACEFA, sun kuma kara da mika goron gayyata ga sauran masu hannu da shunin da ke, da burin bunkasa harkar Ilimi, da su hada hannu da kungiyoyin a cikin wannan aiki.