Business

Gidauniyar Bill Da Melinda Gates Ta Tallafawa Najeriya Da Irin Wake Gagare-Ƙwari

Gidauniyar Bill da Melinda Gates, ta tallafawa Najeriya da irin wake wanda kwari basa kamawa, da nufin bunkasa samar da iri da amfanin gona, a kasar nan.

Babbar Jami’ar shirye-shiryen gidauniyar, wacce ke kasar Amurka, Lawrence Kent, ita ce ta bayyana hakan, yayin da take zantawa da manema labarai, lokacin gudanar da taron bibiyar aikin, ranar Talata, a jihar Kano.

Gidauniyar ta Bill da Melinda Gates, hadin guiwa da Gidauniyar bunkasa fasahar noma su ne suka shirya gudanar taron.

Kent, tace sun zo Kano ne, domin tallafawa aikin na samar da wake wanda kwari basa lalatawa, wanda guda ne cikin manyan al’amuran da gwamnatin Najeriya ta sanya a gaba, hadin guiwa da Gidauniyar Bunkasa Fasahar Noma ta nahiyar Afirka.

A nasa jawabin, Kwamishinan Noma na jihar Kano, Danjuma Mahmud, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren Ma’aikatar, Sadi Ibrahim, ya ce tuni jihar Kano ta shirya rungumar dukkannin abinda da aka cimma a karshen taron, domin bunkasa samar da nau’in waken.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button