Ilimi

Gidauniyar MTN Ta Kashe Biliyan 3 Wajen Bada Tallafin Karatu

Gidauniyar kamfanin sadarwa na MTN (MTN Foundation), ta bayyana cewar, ta kashe sama da Naira biliyan 3, wajen bada tallafin karatu ga Ɗalibai masu ƙarancin galihu, da ke karatun Digirin farko, da ma Ɗalibai masu buƙata ta musamman da ke ƙasar nan.

Daraktan Gidauniyar, Reginald Okeya, shi ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, a ya yin bikin bayar da tallafin karatun da gidauniyar ta bayar, a birnin Fatakwal.

Okeya, ya ce kuɗaɗen wani sashe ne na kuɗin da kamfanin na MTN ya ke warewa, domin bunƙasa rayuwar al’umma, wanda aka shafe sama da shekaru 10 ana gudanarwa.

“Duk shekara gidauniyar nan tana ware wasu kuɗaɗe domin bada tallafin karatu ga masu ƙaramin ƙarfi, makafi, da ma sauran ɗalibai masu buƙata ta musamman.

“Ana gudanar da shirin ne rukuni-rukuni, rukunin yau ya ƙunshi sama da Ɗalibai 300 da su ka fito daga fannonin Kimiyya, waɗanda su ka haɗarda makafi, da sauran masu nakasa.

“Tallafin karatun na Naira 200,000 ne a kowanne zangon karatu (Semester) ga kowanne ɗalibi.

“Ɗaliban da su ka samu nasarar shiga cikin shirin kuma za su cigaba da samun kuɗin, muddin dai sun cigaba da samun sakamakon da bai gaza 3.4 ba (3.4 CGPA) a fannin da su ke karantawa, har su kammala”, a cewarsa.

Su ma wasu daga cikin Ɗaliban da su ka amfana da tallafin sun godewa gidauniyar, tare da yin alƙawarin cigaba da zage damtse dan cimma abin da su ka sanya a gaba.

Daga cikin manyan baƙin da su ka halarci rabon tallafin kuma, akwai Shugaban Jami’ar ta jihar Niger, Farfesa Nlerum Okogbule, da Wakilin Jami’ar Fatakwal, da sauran manyan mutane.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button