Ilimi

Ginin Makarantun Firamare 3 Zai Laƙume Biliyan 1.5 A Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta ware Naira biliyan 8, dan gina sababbin makarantun firamare na zamani, a jihar.

A cewar Gwamna, Abba Kabir Yusuf dai, za a samar da wadatattun kayayyakin koyo da koyarwa a makarantun, wanda hakan zai bada kyakykyawan yanayi ga daliban da ke fitowa daga gidajen talakawa ta fuskar amfana da ingantaccen Ilimi daga tushe, da nufin haskaka gobensu.

Gwamnan, ya kuma ce manyan makarantun guda uku, za a samar da su ne a kowacce guda daga cikin gundumomin jihar, wadanda za su kasance kawace da wadatattun kayayyakin koyo da koyarwa, dan wanzar da nagartaccen Ilimi a matakin farko.

Ka zalika, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce Gwamnatinsa ta amince da sabunta makarantu na musamman guda 26 da Gwamnatin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ta samar, inda tuni aka kammala aikin guda 17 daga ciki.

Bugu da kari, Gwamnan ya kara da bayyana cewar, Gwamnatinsa ta biya kimanin Naira miliyan 700 na kudaden rijistar Daliban Jami’ar Bayeero, da ke birnin Kano, ya yin da a gefe guda ta kashe kimanin biliyan 1.5 wajen biya wa dalibai kudaden rijistar jarrabawoyin WAEC da NECO.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button