Gobara Ta Mamaye Wani Sashe Na Kamfanin Robobi, A Lagos
Wani sashe a masana’antar sarrafa robobi, da ke jihar Lagos, ya kama da wuta, a ranar Asabar.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta Lagos, ita ce ta bayyana hakan ta cikin wani jawabi da Daraktan hukumar, Adeseye Margaret, ya sanyawa hannu.
Jawabin wanda aka wallafa a shafin hukumar na X, ya kuma bayyana cewar, Jami’an hukumar sun halarci wurin da gobarar ta auku.
Ga abin da jawabin ke cewa, “Hukumar kashe gobara ta jihar Lagos, a yanzu haka ta na yunƙurin kashe gobara da ta kama a kamfanin Mega Plastic, da ke Illupeju bypass, Mushin, a Lagos.
“Mun samu sanarwar gaggawa game da aukuwar lamarin, da misalin ƙarfe 07 da mintuna 26 na ranar Asabar, kuma ofisoshin hukumar kashe gobara na Illupeju, Bolade, da ma Alausa, sun samu halartar wurin da lamarin ya faru, inda su ke ƙoƙarin kashe gobarar a yanzu haka.
“Gobarar ta shafi sashen ajiya, da ma fannin adana Sinadarai na kamfanin, a ya yin da aka kusa shawo kanta. Zuwa yanzu kuma, babu rahoton jikkata, ko rasa rai, sanadiyyar aukuwar lamarin”.
Ka zalika, a cikin ta ta sanarwar ta daban, hukumar kula da harkokin tuƙi ta jihar Lagos (LASTMA), ta ce gobarar wacce aka samu da safiyar yau Asabar, ta shafi sashen ajiya da wasu fannoni na kamfanin, sai dai ba a samu asarar rayuka, ko jikkata ba.