Siyasa

Gwamnan Jihar Gombe, Ya Karɓi Takardar Shaidar Lashe Zaɓe

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, tare da Mataimakinsa, Dr. Manassa Jatau; da ma ƴan Majalissar Dokokin jihar kimanin 24 sun karɓi shaidar lashe zaɓensu, a yau (Alhamis).

Da ya ke jawabi, jim kaɗan bayan karɓar takardar shaidar, daga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Gwamna Yahaya, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su zo su haɗa hannu da Gwamnatinsa, dan ganin an ciyar da Jihar gaba.

Yana mai cewar, tsarinsa a siyasa ba nasa ne shi kaɗai ba, kuma sam babu wanda ya yi nasara da wanda ya faɗi.

Ka zalika, ya kuma ƙara da cewar, akwai buƙatar dukkannin sauran ƴan takarkarun da su ka yi rashin nasara su haɗa hannu da shi, domin ciyar da Jihar Gombe gaba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button