Labarai

Gwamnan Kano Ya Ƙaddamar Da Shirin Rabon 50,000 Kowanne Wata, Ga Mata 5,200

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da shirin fara rabon Naira Dubu Hamsin-Hamsin ga Mata 5,200 da ke yankunan ƙananan hukumomin jihar guda 44.

Bayanin hakan, na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da Gwamnan ya wallafa, a shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook, da yammacin Talata.

Gwamnan ya ce, za a dinga kashe kimanin Naira miliyan 260 a kowanne wata, wajen tallafawa mata da Naira 50,000 ɗin, har ƙarshen wa’adin mulkinsa.

Ya ce, shirin wanda hukumar CRC za ta dinga gudanar da shi, zai tallafawa mata Ɗari-Ɗari a kowacce ƙaramar hukuma, daga cikin ƙananan hukumomi 36 na wajen birnin jihar, da kuma mata Ɗari Bibbiyu daga kowacce ƙaramar hukuma da ke cikin ƙananan hukumomin ƙwaryar birnin jihar guda 8.

Abba, ya ce sun Samar da shirin tallafin ne, domin nuna godiyarsu ga irin gagarumar gudunmawar da mata su ka basu, a yayin zaɓen 2023 da ya gabata.

Ga abin da jawabin na Abba Gida-Gida ke cewa, “A kokarin gwamnatinmu na inganta kananu da matsakaitan sana’oi a Kano, yau na kaddamar da shirin tallafawa mata, wanda zaa rika zabo a kalla mata 5,200 a fadin jahar ana tallafawa kowannensu da jarin Naira dubu hamsin-hamsin.

“Zaa ci gaba da rabawa mata daban-daban daga dukkanin kananun hukumomi 44 na jihar Kano wadannan kudade, wanda jumullarsu ya kai Naira miliyan 260, duk wata daga wannan lokaci har zuwa lokacin da wa’adin mulkina zai cika.

“Wannan shiri, wanda hukumar CRC ce zata rika gudanar da shi, zai tallafawa mata dari-dari daga kowace karamar hukuma a cikin kananun hukumomi 36 na wajen birnin Kano, da kuma mata dari biyu-biyu daga kowace karamar hukuma a cikin kananun hukumomi 8 na cikin birni.

“Ina jaddada cewa wannan shiri na tallafi mun yi shi ne don nuna godiyar mu ga mata saboda gagarumar gudunmawar da suka bamu da jajircewar da suka yi don ba mu goyon baya a zaben da aka yi na shekarar 2023.- AKY”, a cewarsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button