Labarai
Gwamnan Kano Ya Aike Da Ƙarin Sunayen Da Ya Ke Son Naɗawa A Matsayin Kwamishinoni
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da sunayen mutanen da ya ke fatan ƙara naɗawa a matsayin Kwamishinoni, ga Majalissar Dokokin jihar.
Sunayen waɗanda Gwamnan ya aikewa majalissar a ranar Talata domin tantancewa sun haɗar da: Engr. Kabir Jibrin, Alhaji Shehu Muhammad Na’Allah Kura, da Isyaku Ibrahim Kunya.
Sauran su ne: Dr. Salisu Muhammad Tudun Kaya, Amina Inuwa Fagge, da Garba Ibrahim Tsanyawa.
Ku cigaba da kasancewa da Jaridar Rariya Online, a wannan shafi namu na https://matatarlabarai.com, za mu zo da cikakken bayani.