Gwamnan Kano, Ya Naɗa Sababbin Muƙamai, Tare Da Bada Umarnin Ƙwace Kadarorin Da Ganduje Ya Cefanar
Sabon Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa muƙamai na farko a gwamnatinsa, jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin Gwamnan jihar.
Da safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023 ne dai, Mai Shari’a Dije Aboki, ta rantsar da zaɓaɓɓen Gwamnan a matsayin sabon Gwamnan Kano mai cikakken iko, inda kuma ya fara Aiki nan take.
Daga cikin sababbin muƙaman da Gwamnan ya naɗa akwai:
1. Hon. Shehu Wada Sagagi, a matsayin Shugaban Ma’aikata (Chief of Staff).
2. Abdullahi Baffa Bichi, PhD, a matsayin Sakataren Gwamnati (Secretary to the State Government).
3. Dr. Farouq Kurawa, a matsayin
Principal Private Secretary.
4. Sai, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, da aka naɗa Chief Protocol.
5. Da Sanusi Bature Dawakin Tofa, da ke matsayin Sakataren yaɗa labaran Gwamnan (Chief Press Secretary).
Bayanin naɗin kuma, ya fito ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya sanyawa hannu, wacce ta bayyana cewar sababbin muƙaman za su fara aiki ne daga ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 (nan take).
A gefe guda kuwa, Gwamnan ne ya umarci Jami’an tsaro, da su karɓe kadarorin da tsohuwar Gwamnatin jihar Kano (ta Ganduje) ta sayar ba bisa ƙa’idaba, ga ƴan uwansu da ƴaƴansu.
Abba, ya kuma bada wannan umarni ne ta shafinsa na Facebook, cikin wata sanarwa da ya wallafa jim kaɗan bayan rantsar da shi.
Ya na mai cewar, ”Bisa la’akari da shawarar da kwamatin ƙarbar mulki ta bamu, nake sanar da cewa. Daga wannan rana, duk wasu filayen jama’a da kadarorin da gwamnatin Ganduje ta wawashe tare da siyar da su jami’an tsaro su karɓe su har sai lokacin da gwamnati za ta yanke hukunci a kansu.”
”Mun lura da cewa gwamnatin da ta shuɗe ta sayar da filaye a makarantu, gidajen tarihi, masallatai, asibitoci, maƙabartu da wuraren hutawar jama’a, da kuma gefen ganuwar birnin Kano. Mun kuma lura da cewa sun siyar da kadarorin gwamnatin jihar Kano masu yawa a ciki da wajen jihar nan ga ƴan uwansu da ƴaƴansu ba bisa ƙa’ida ba. – AKY”.