Gwamnan Kogi Ya Amince Da Ninka wa Masu Hidimar Ƙasa Ƙuɗaɗen Alawus
Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amince da yin ƙarin kaso 100 akan kuɗaɗen alawus-alawus ɗin masu hidimar ƙasa a Jihar, na wata-wata.
Bello, ya sanar da wannan ƙari ne, ranar Talata, a sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima da aka turo Jihar, domin gudanar da hidimar ƙasar su, na tsawon shekara guda.
Gwamnan ya ce, Gwamnati ta amince da wannan ƙari ne, duba da irin halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi, da ma ganin alfanun tsarin na hidimar ƙasa da Gwamnati ke yi, ta fuskar ƙara haɗakan al’ummar ƙasar nan.
Ya kuma ce, masu yi wa ƙasa hidimar na bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban Jihar ta Kogi, da ma ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan kuma, shi ne ya kasance babban baƙo, a ya yin bikin rufe sansanin masu yi wa ƙasa hidima na Asanya, da ke ƙaramar hukumar Kabba Bunu, a rukunin B na shekarar 2023.
Ya kuma sanar da bayar da tallafin Naira miliyan Talatin da Bakwai ga Matasan ƴan hidimar ƙasar, tare da buƙatar su yi amfani da kuɗaɗen wajen zuwa wuraren da aka tura su.
Ya kuma buƙaci mamallaka kamfanoni masu zaman kansu, da su tabbatar da walwalar masu hidimar ƙasar a kamfanoninsu.
Inda su ma Matasan, ya buƙace su da su kasance masu ɗa’a, da ma nuna kyawawan halaye, ba tare da alamta banbancin Addini ko ƙabila ba.
Jimillar masu yi wa ƙasa hidimar da aka aike zuwa Jihar ta Kogi dai su ne, 1,888, wanda ya haɗar da Maza 977, da Mata 911.