Gwamnati Na Barazanar Soke Lasisin Kamfanonin Rarraba Lantarki
Gwamnatin tarayya, ta yi barazanar soke lasisin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarkin da ke ƙasar nan, sakamakon tsanantar matsalar ƙarancin wuta da dukkannin ɓangarorin ƙasar ke fama da ita.
Ministan lantarki, Adebayo Adelabu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Ministan, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta X, ya ce tuni su ka yi sammacin shuwagabannin Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki Na Babban Birnin Tarayya Abuja, da na Ibadan, tare da Daraktan gudanarwa na kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasa.
Ministan ya kuna sha alwashin bunƙasa tsarin amfani da na’urar meter, ba ya ga bunƙasa samuwar wutar lantarkin, tare da tilastawa Discos rarrabata ga al’umma da kamfanonin ƙasa.
Bugu da ƙari ya ce, tuni shirye-shirye su ka yi nisa na biyan dukkannin kamfanonin samar da gas kuɗaɗen basussukan da su ke bi.