LabaraiUncategorized

Gwamnati Ta Amince Da Ƙarawa Malaman Manyan Makarantu Albashi

Gwamnatin tarayya ta amince da aiwatar da ƙarin kaso 35 da kaso 23 na kuɗaɗen Albashi, ga Ma’aikatan manyan makarantun ƙasar nan.

Bayanin hakan na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da hukumar kula da Al’amuran Albashi da kuɗaɗen shiga ta ƙasa ta fitar, mai kwanan watan 14 ga watan Satumba, wacce kuma ke ɗauke da sa hannun Shugabanta, Ekpo U. O. Nta.

Sanarwar ta kuma ƙara da bayyana cewar, za a biya dukkannin ma’aikatan kuɗaɗensu na Ariyas, wanda ya fara daga ranar 1 ga watan Janairun 2023.

Wannan ƙarin Albashi kuma, zai shafi Ma’aikatan da ke Jami’o’i, Kwalejojin Ilimi (Colleges Of Education), da ma Kwalejojin Fasaha (Polytechics) ne.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button