Wasanni

Gwamnati Ta Bawa Kano Pillars Wa’adin Wasanni 3

A ranar Juma’a ne, gwamnatin jihar Kano, wacce ke da mallakin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ta bawa hukumar gudanarwa, da ma’aikatan ƙungiyar wa’adin wasanni uku, da su taka rawar a zo a gani.

A yayin da ya ke bayyana basu wannan wa’adi, Kwamishinan riƙo, na Ma’aikatar Matasa da Wasanni, Hamza Kachako ya ce, an bawa ƙungiyar wannan wa’adi ne, domin ta ɗauki hanyoyin da za su kaita ga nasara.

Sai dai, bai bayyana abin da zai iya faruwa ga shuwagabanni, ko ita kanta ƙungiyar ba, idan ta gaza yin abin da ya dace, a cikin wannan wa’adi.

Bada wannan wa’adi ga ƙungiyar kuma, yana da nasaba da gaza taɓuka abin kirki da ƙungiyar tayi, a gasar Premier ta ƙasa, ta kakar 2023/2024 da ke cigaba da gudana.

Kwamishinan, ya ƙara da bayyana ƙoƙarin gwamnatin Kano, wajen bunƙasa ƙungiyar ta Pillars, ta hanyar bata dukkannin wata gudunmawa da take da buƙata, dan cimma gaci.

Kano Pillars, za ta sake fafata wasanta na gaba ne, tsakaninta da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Gombe United, ranar Lahadi, a buɗaɗɗen filin wasa na Sani Abacha, da ke birnin Kano.

A yanzu kuma, Kano Pillars na a matsayi na bakwai ne, a teburin gasar ta Premier, inda take da maki 41, a wasanni 30 da ta buga.

Ko a wasanta na ƙarshe da ya gudana ma dai, Kano Pillars ɗin rashin nasara tayi, a hannun Bendel Insurance ta Benin, da ci 1 da 2.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button