Labarai
Gwamnati Ta Fara Rabon Gidaje Ga Ƴan Ƙasa
Gwamnatin tarayya ta fara gudanar da aikin rabon gidaje akan sassauƙan farashi, ga al’ummar ƙasar nan, da ke da sha’awa.
Babban Kwantirolan kula da rabon gidajen Gwamnatin tarayyar reshen Adamawa, Martin Gyado, shi ne ya tabbatar da hakan, a ya yin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ranar Juma’a, a birnin Yola.
Gyado, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bunƙasa shirin rabon gidajen ta hanyar ƙara samar da wasu birane na musamman.
Inda ya ce, gidajen da ake tsaka da rabawa a yanzu, Gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ce, ta samar da su.
Ya kuma ce, dukkannin masu buƙata za su iya halartar ofisoshin Kwantirolan jihohinsu, domin mallakar Application Forms, a kyauta.