Ilimi

Gwamnati Ta Haramta wa Yara Masu Ƙarancin Shekaru Rubuta Common Entrance

Ma’aikatar Ilimi ta Gwamnatin tarayya, ta gargaɗi Iyaye, da ma masu kula da yara, da su ƙauracewa yi wa yaran da ke da ƙarancin shekaru, rijistar jarrabawar Common Entrance. Inda ta bayyana basu damar rubuta jarrabawar a matsayin abin da ke da hatsarin gaske, tare da shan alwashin ɗaukar ƙwararan matakai, wajen ganin ba a bawa irin waɗancan ɗalibai guraben karatu, a makarantun Sakandiren haɗaka (Unity Schools) ba.

Babban Sakataren ma’aikatar, Andrew Adejoh, shi ne ya bayyana hakan, ranar Asabar, a babban birnin tarayya Abuja, ya yin da ya ke gudanar da zagayen sanya ido, kan yadda ake rubuta jarrabawar kammala makarantun firamaren ta Common Entrance, domin shiga makarantun haɗaka, a kakar karatu ta 2023.

Hukumar shirya jarrabawa ta NECO ce dai, ta ke gudanar da jarrabawar a kowacce shekara, ga ɗaliban da su ka bayyana sha’awarsu, inda a wannan shekarar kimanin Ɗalibai 72,821, daga sassa daban-daban na ƙasar nan, su ka yi rijistar jarrabawar.

A lokacin zagayen an jiyo Adejo dai, ya na cewa, ”A wannan shekarar, ina roƙon Iyaye da su yi amfani da shawarar da mu ke bayarwa. Muna kashe yaranmu ne, ta hanyar barin masu ƙarancin shekaru daga cikinsu su na rubuta jarrabawar Common Entrance. Ni naga yaran da ba su haura shekaru 10 ba, da yawa sun je rubutuwa, uku daga cikin su ma sun ce min shekarunsu tara-tara, ina son mu sani muna ɗora yaranmu akan hanyar da ba mai ɓullewa bace. Bacin jarrabawa bane Ilimi. Ilimi shi ne koyarwa, koyo, da kuma gina tarbiyya.

”Ina roƙon Iyaye; da su dinga bawa yaransu damar rubuta jarrabawar nan, amma idan shekarun su sun kai. Babu wata ƙaruwa da zamu samu ta hanyar sanya yaranmu su yi zuƙu (karatun wuri). A mafi yawan lokuta ma, idan yaro ya yi komai a ƙananan shekaru, to ya na fuskantar matsala nan gaba, a rayuwarsa. Saboda haka an tsara Ilimi ne dai-dai da kowanne mataki na rayuwa, akwai saƙonnin da ƙwa-ƙwalenmu za su iya ɗauka, su fahimta, su kuma iya yin amfani da su.

”Saboda haka, a wannan yanayi, idan ku ka dage har yaranku su ka ci wannan jarrabawa, su ka shiga sakandire, har su ka kammala ma, to kuwa shiga Jami’a zai zame musu matsala. Na ga hakan daga kan wani Abokina. Har yanzu yaransa sun gaza shiga Jami’a, kawai saboda sun shiga makarantun haɗaka da ƙananan shekaru”.

Ya kuma ce, Gwamnatin tarayya za ta tabbatar da cewar hukumar NECO ɗin ta sanya lura, wajen ajiye ƙwarya a gurbinta, ya yin bada guraben karatu, ta hanyar gudanar da tantancewar ƙeƙe da ƙeƙe, ko ma a sa yaran su kai takardun haihuwarsu.

Ya kuma ce, ƙudirin Gwamnatin tarayya, da sauran masu ruwa da tsaki na haɓɓaka Ilimin yara mata, ya na samun tagomashi, bayan da ya ce kimanin yara mata 38,000 ne su ka yi rijistar jarrabawar, wanda adadin ya shallake na shekarar da ta gabata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button