Kasuwanci

Gwamnati Za Ta Fara Karɓar 600,000 Daga Masu Motoci, Domin Mayar Da Su Masu Amfani Da Gas

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar, ana tsammanin al’ummar Najeriya za su dinga biyan tsakanin Naira 300,000 da 600,000, domin sauya Motocinsu daga tsarin amfani da Man_Fetur, zuwa iskar Gas ta CNG.

Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa, kan sauya Ababen Hawa Zuwa Masu Amfani Da Iskar Gas (P-CNGi), Engr. Michael Oluwagbemi, shi ne ya bayyana hakan, a ya yin zantawarsa da Manema Labarai, jim kaɗan bayan ƙaddamar da Cibiyoyin sauya ababen hawan zuwa masu amfani da CNG, haɗin guiwa da kamfanoni masu zaman kansu, a ofishin rukunin kamfanonin Femadec, da ke Lagos, wanda guda ne daga cikin kamfanonin da su ka haɗa guiwa da Gwamnatin tarayya, domin gudanar da wannan Aiki.

Shugaban, ya kuma bayyana shirin Gwamnatin tarayyar na samar da Cibiyoyin sauya ababen hawan zuwa masu amfani da Gas kimanin 10,000 a nan kusa.

Ya kuma ce, fara aikin sauya ababen hawan daga masu amfani da Fetur zuwa Iskar Gas, abu ne da zai taka gagarumar rawa, wajen bunƙasa samuwar ayyukan yi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button