Gwamnatin Borno Ta Buɗe Shafin Neman Tallafin Karatu
Hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, ta buɗe shafin neman tallafin a kakannin karatu na 2022/2023 da 2023/2024, ga ɗaukacin ɗaliban Jihar da ke karatu Manyan Makarantun ƙasar nan.
Da ya ke tabbatar da cigaban ga kamfanin dillancin Labarai na ƙasa, a birnin Maiduguri, Babban Sakataren hukumar, Mallam Bala Isa, ya ce an buɗe shafin ne a ranar 14 ga watan Satumban da mu ke ciki, za kuma a rufe ne a ranar 14 ga watan Oktoba.
“Dukkannin Ɗalibai ƴan asalin jihar Borno, da su ka samu guraben karatu a manyan makarantun Najeriya, kuma sun yi rijista da makarantun a shekararsu ta farko, su na da damar su nema.
“Ɗaliban da ke sha’awa, za su iya cikewa, ta shafin, scholarship.bo.gov.ng.
“Muna shawartar Ɗalibai da su sanya lura, a lokacin da su ke cikewa, domin babu ƙorafin da zamu karɓa kan yin rijista ba dai-dai ba”, a cewarsa.
Kamfanin dillancin Labarai na ƙasa, ya rawaito cewar Gwamnatin jihar ta Borno, na bayar da tallafin karatu ga Ɗaliban Manyan Makarantun gaba da Sakandire, kamar Jami’o’i, Makarantun Samun Horon Zama Lauya, Kwalejojin Fasaha, da ma Kwalejojin Ilimi.