Gwamnatin Buhari Ta Samar Da Ayyukan Yi, Miliyan 12 – Fadar Shugaban Ƙasa
Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman, kan al’amuran yaɗa labarai, Garba Shehu, ya bayyana cewar, Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta samar da ayyukan yi, kimanin miliyan 12, a fannin Noma kaɗai.
A ya yin zantawarsa da tashar Talabijin ta Channels, cikin shirin Sunrise Daily, a ranar Talata, Garba Shehu, ya ce, Gwamnatin tasu ta yi abin bajinta a fannonin tsaro, makamashi, yaƙi da rashawa, da makamantansu.
”A fannin noma kaɗai ƙungiyar Manoma Shinkafa ta ƙasa (RIFAN) tana batu ne kan samar da ayyukan yi miliyan 12, ku duba dai abin da muka yi wa noma, Gwamnatin mu ta gaji kamfanonin samar da taki guda huɗu ne kacal da su ke aiki, amma yanzu muna da guda 52.
”Kuma fa waɗannan sababbin manoman shinkafar miliyan 12, mun samar musu da wadataccen taki, kawai dan samar da shinkafa ƴar gida. A yanzu ƙasar nan ta cimma matakin da ta ke iya ciyar da kanta, wanda hakan abu ne da ya ke bunƙasa tattalin arziƙi.
”A baya, ƙasar nan na kashe Dalar Amurka biliyan 5 ne a kullum, domin sayo shinkafar waje kawai, amma a yanzu ko Dalar Amurka ɗaya ba a fitarwa, domin sayo shinkafa.
A ɓangaren yaƙi da rashawa ma, Garba Shehun ya ce sammakal, domin kuwa a yanzu babu wani asusun banki, wanda ke ɗauke da kuɗaɗen sata, da ya ke aiki.