Gwamnatin Jigawa Ta Sanya Hannu Kan Yarjejeniya Da ITF, Domin Samarwa Matasa Ayyuka
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu akan yarjejeniyar fahimtar juna da Asusun horaswa na Masana’antu (ITF), da nufin samar da Ayyuka ga Matasan jihar masu tasowa.
A ya yin sanya hannun dai, Gwamna Namadi, ya kuma sha alwashin kasancewa Jakadan Asusun na ITF a zauren Gwamnonin Najeriya (NGF), inda ya bayyana samarwa da Matasa Ayyuka a matsayin abin da Gwamnatinsa ke bawa muhimmanci na farko-farko.
Malam Namadi, wanda kuma ya bayyana damuwarsa kan yawaitar Matasan da basu da Ayyukan yi, a faɗin ƙasar nan, da ma halin matsin da tattalin arziƙin ƙasa a ke ciki, ya ce, “Babbar matsalar da na koka akanta tun a ya yin da na ke yaƙin neman zaɓe, da naga fitowar Matasa gungu-gungu ita ce rashin Aikin yin Matasa. Wacce ta daɗe ta na cimin tuwo a ƙwarya, domin dole ne a kawo ƙarshenta.
“Haƙƙinmu ne baki ɗaya mu kula da Matasa. Hakan ne ma ya sa mu ke son samar da hukumar samarwa da Matasa Ayyukan yi, tare da kashe narka maƙudan kuɗaɗe akanta, dan ganin mun cimma Manufarmu akan matasan Jigawa”, a cewarsa.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Asusun na ITF, Mr. Joseph N Ari, ya bayyana godiyarsa ga Gwamnatin Jihar ta Jigawa, bisa ƙulla alaƙa da su, wajen ganin an samar da Matasa masu amfani, a Jihar.