Gwamnatin Kaduna Na Shirin Fara Biyan Ƴan Fanshon Da Basu Da Asusun Banki
Hukumar kula da haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikata, ta jihar Kaduna (Kaduna State Pension Bureau), ta bayyana cewar, tuni ta fara ɗaukar matakan biyan tsofaffin ƴan fansho, da ma mutanen da su ka rasa rayukan su, waɗanda basu da asusan bankuna.
Babban Sakatariyar hukumar, Farfesa Salamatu Isah, itace ta bayyana hakan, ta cikin wani jawabi da ta fitar, ranar Alhamis, a Kaduna.
Inda tace, Jami’an ƙananan hukumomi ne za su tantance, tare da biyan tsofaffin ma’aikatan haƙƙoƙinsu, ya yin da takwarorinsu kuwa, za a tantancesu a ma’aikatu, sassa, da ma hukumomin da suka bari.
Salamatu ta kuma ce, kimanin ƴan Fansho 112 ne, za su amfana da wannan tsari a ƙarƙashin rukunin hukumar na 21 (Batch 21), ya yin da sauran 134 kuwa, za su amfana ne a ƙarƙashin rukunin ƙananan hukumomi na 19.
Sakatariyar ta kuma ce, za a tantance, tare da biyan haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikatan, a helikwatar shiyyoyi ne, a makon gobe.
Ka zalika, ta kuma ce, Gwamnatin jihar ta ware kimanin Naira miliyan 920 domin biyan haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikatan, da ma waɗanda su ka rasa rayukan su.
Inda aka samar da sama da Naira miliyan 400 domin biyan ƴan fanshon jihohi, ya yin da Naira miliyan 520 kuwa aka wareta domin biyan ƴan Fanshon da ke a matakan ƙananan hukumomi.