Gwamnatin Kaduna Ta Gwangwaje Ɗalibin ABU Mafi Ƙwazo Da Takardar Aiki
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya gwangwaje haziƙin Ɗalibin nan na Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zaria, Abu-Hurairah Mahadi, da takardar ɗaukar aiki kaitsaye, bayan da ya kammala Jami’ar da sakamako ajin farko (First Class), tare da kasancewarsa Ɗalibin da ya fi kowanne Ɗalibi yawan maki.
Ka zalika, Gwamnan ya kuma ɗauki nauyin karatun Digirin farko, ga Nasara James Dabo, wacce Ɗaliba ce mai shekaru 14 da ta nuna hazaƙa ta musamman a gasar Lissafi ta ‘Mathematics Genius ‘.
Ta cikin jawabin da Sakataren yaɗa labaransa, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, Gwamnan ya bayyana cewar, “Gwamnatin Kaduna ta bada takardar ɗaukar aiki kaitsaye, ga Abu-Hurairah Mahadi, wanda Ɗalibi ne da ya kammala karatun Digirinsa na farko, da daraja ta ɗaya (First Class), a Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zaria, tare da Nasara James Dabo, wacce Ɗaliba ce da ita ma ta nuna matuƙar ƙwazo a gasar Lissafi, inda shi ma aka ɗauki nauyin karatunsa na Digirin farko.
“Abu-Huraira Mahadi ya kasance Ɗalibi mafi ƙwazo a cikin dukkannin Ɗaliban da su ka kammala Jami’ar ta ABU a wannan shekarar, bayan da ya kammala da CGPA 4.95, kuma shima gwamnatin Kaduna ta ɗauki nauyin karatunsa na Digiri na biyu (Master’s Degree), a dukkan Jami’ar da ya zaɓa, a faɗin duniya, ciki kuwa harda Harvard da Cambridge.”.