Zamantakewa

Gwamnatin Kaduna Ta Jaddada Matsayarta Na Dandaƙe Masu Fyaɗe A Jihar

Gwamnatin jihar Kaduna, ta bayyana cewar, babu gudu – ba ja da baya, kan ƙudurinta na dandaƙe dukkannin mutumin da aka samu da laifin aikata fyaɗe, a jihar.

Kwamishiniyar Inganta rayuwar al’umma ta jihar, Hajiya Rabi Salisu, ta ce hukuncin yin dandaƙa ga Maza da Matan da aka samu da aikata laifin fyaɗen ya zo dai-dai da tanadin dokar hana cin zarafi ta jihar, ta shekarar 2018, wacce aka samar domin kawo ƙarshen fyaɗe da cin zarafin jinsi a faɗin jihar.

Gwamnatin Kaduna, ta samar da dokar ne dai, bayan taɓa-alli da hukumomi, da dukkannin ɓangarorin da lamarin ya shafa.

Tun bayan sahalewa dokar kuma, tuni gwamnatin jihar ta shiga aikin wayar da kan al’umma kan Illolin fyaɗen, da nufin ganin an ƙauracewa aikata shi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button