Gwamnatin Kaduna Za Ta Horas Da Mata 5,000 Kan Dabarun Amfani Da Ƙirƙirarriyar Fikira
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewar, Gwamnatinsa ta mayar da hankali kan amfani da fasahar ƙirƙirarriyar fikira (Artificial Intelligence), da Saƙago (Robotics).
Sani, ya bayyana hakan ne, ranar Talata, ya yin da ya ke ƙaddamar da taron bajakolin ƙirƙirarriyar basirar da saƙago, karo na 3, ranar Talata, a Kaduna.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Dr. Hadiza Balarabe, ya ce gwamnatinsa ta ƙarfafa fannin amfani da fasahar zamani, dan bunƙasa rayuwar al’ummar jihar.
Ya kuma ƙara da bayyana cewar, gwamnatin jihar ba za ta yi sake a bar al’ummarta a baya ba, ta fuskar fasahohin AI da Robotics ɗin, waɗanda kasuwarsu ke cigaba da sharafi a faɗin duniya.
Ya kuma ce, tabbas zamani zai bar dukkannin mutanen da su ka gaza rungumar tagwayen fasahohin.