Gwamnatin Kano Na Shirin Dawo Da Harajin Masu Adai-daita Sahu, Da Sabunta Rijista
Gwamnatin jihar Kano, ta bayyana cewar, shirye-shirye sun yi nisa, wajen dawo da biyan harajin kullum-kullum ga matuƙan baburan Adai-daita Sahu, a Jihar.
Kwamishinan Sufuri, Injiniya Muhammad Diggol, shi ne ya bayyana hakan, da yammacin ranar Juma’a, ya yin da ya ke jawabi, a helikwatar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta KAROTA, ya yin ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin sufurin baburan na adai-daita sahu, a Jihar nan.
Inda ya ce, wajibi ne, Gwamnati ta cigaba da karɓar kuɗaɗen harajin, muddin dai ana son ciyar da Jihar Kano gaba, ta fuskar sufuri.
Kwamishinan, ya kuma ƙara da cewar, nan ba da jimawa ba, za a sabunta rijistar Adai-daita Sahu, domin tantance matuƙansu, da ma tantance haƙiƙanin adadinsu.
Ya kuma yi albishirin cewar, Gwamnati za ta fito da sababbin tsare-tsare, da za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin na kullum-kullum, da ma sabunta rijistar, ba tare da an musguna musu ba, duba da halin matsin rayuwar da ake ciki.
A yanzu kuma, wajibi ne ya kowanne maƙin Adai-daita, ya samu sanya hannun Mai Unguwarsu, kafin Gwamnati ta yi masa rijista, duba da yadda hakan zai taimaka wajen inganta tsaro, a faɗin jihar baki ɗaya.