Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kano Na Shirin Samar Da Cibiyar Daƙile Cututtuka

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da wasiƙa gaban majalissar dokokin jihar, inda ya ke buƙatar ƴan majalissar da su sahale masa samar da hukumar daƙile cututtuka.

Sugaban majalissar, Jibril Isma’il Falgore ne, ya karanta wasiƙar , a ya yin zaman majalissar na ranar Litinin.

Wani jawabi da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Majalissar, Uba Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewar, wasiƙar ta ƙara da bayyana yadda samar da cibiyar zai taka gagarumar rawa wajen kawo ƙarshen matsalar ɓarkewar cututtuka da ake yawan fuskanta, a jihar.

Ka zalika, Majalissar ta kuma karɓi rahoto daga Kwamitin kula da harkokin zaɓenta, kan batun tantance, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, da gwamatin Kanon ke fatan naɗawa a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (KANSIEC).

Rahoton, wanda shugaban masu rinjaye na Majalissar, Lawan Hussaini Dala, ya karanta, ya bayyana cewar, Kwamitin ya aminta da dacewar Farfesan kan wannan muƙami da ake fatan naɗa shi.

Majalissar, ta kuma ɗage cigaba da zamanta, zuwa ranar Talata, bayan wani ƙudiri da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala, ya gabatar, wanda ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye, Labaran Abdul Madari.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button