Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Biyan Ƴan_Fansho Haƙƙoƙinsu Na Garatuti
Gwamnatin jihar Kano, ta ƙaddamar da biyan tsofaffin ma’aikata haƙƙoƙinsu na barin Aiki (Garatuti) a yau (Asabar), 2 ga watan Disamban 2023.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci ƙaddamar da biyan kuɗin ga ƴan fansho sama da 5,000, tare da Iyalan waɗanda su ka rasa ransu daga ciki.
Bikin ƙaddamarwar wanda ya gudana, a ɗakin taro na Coronation Hall, da ke gidan Gwamnatin Kano, ya samu halartar ɗumbin tsofaffin ma’aikata.
Hakan kuma na daga cikin matakan da sabuwar Gwamnatin ta Kano ke cigaba da ɗauka, da nufin ganin ta gyara kura-kuran da take zargin jam’iyyar APC da aikatawa, lokacin da ludayinta ke kan damo, na riƙe haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikata.
A ya yin taron dai, an jiyo Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na bayyana cewar, kuɗaɗen da aka biya, haƙƙin ma’aikatan ne, ba alfarma aka yi musu ba, kuma sun cancanci fiye da haka ma, duba da tsawon lokacin da su ka shafe su na gudanar da aikin raya jihar Kano.
Daga cikin tsofaffin ma’aikatan da su ka rabauta da biyan kuɗaɗen Garatutin dai, akwai waɗanda su ka shafe sama da shekaru Tara da kammala Aiki, ba tare da an biya su haƙƙoƙinsu ba.