Labarai

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Naɗe-Naɗe A Masarautun Jihar

Gwamnatin Kano, ta bada umarnin dakatar da dukkannin wani nau’i na naɗin Sarauta, a ɗaukacin Masarautun jihar guda 5, har sai abin da hali ya yi.

Bayanin hakan na ɗauke ne, ta cikin wata wasiƙa da aka aike ga ɗaukacin Masarautun jihar, wacce kuma ke ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar kula da al’amuran ƙananan hukumomi, Ibrahim Kabara.

Idan za a iya tunawa dai, ko a ranar 2 ga watan Fabrairu ma, sai da Gwamnatin jihar ta dakatar da Masarautar Bichi daga naɗa, Salisu Ado Bayero, a matsayin Hakimi.

Kano nada Masarautu guda biyar ne, da su ka haɗar da; Masarautar Kano, Masarautar Gaya, Masarautar Rano, Masarautar Bichi, da Masarautar Ƙaraye.

Wasiƙar da gwamnati ta aikewa Masarautun, mai ɗauke da kwanan watan 28 ga watan Fabrairu ta ce, an ɗauki matakin ne sakamakon tarin matsalolin da ake fuskanta.

Wasiƙar ta kuma buƙaci Masarautun da su dinga aikewa da dukkannin buƙatunsu na gudanar da wani abu ga Ofishin Kwamishinan Ƙananan hukumomi, domin samun sahalewa, kafin su zartar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button