Labarai

Gwamnatin Kano Ta Fara Aikin Gyaran Hanyoyin Ruwan Da Ambaliya Ta Lalata

Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta fara aikin sake gina Kwalabatin Danya, Kwakwaci, da ke ƙaramar hukumar Gwarzo, bayan da ta rufta sakamakon gagarumar ambaliyar ruwan da aka fuskanta, a daminar da ta gabata.

Hukumar kula da gyara titunan jihar Kano ta KARMA ce, ke gudanar da aikin sake gina kwalabatin, wacce ta shafe tsawon shekaru.

Aikin kwalabatin kuma, guda ne daga cikin ɗumbin ayyukan da Gwamnatin jihar ke gudanarwa, na sake inganta hanyoyi da magudanan ruwan jihar, waɗanda ambaliyar ruwan sama ta lalata, a daminar da ta gabata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button