Gwamnatin Kano Ta Kai Ɗaliban Sakandire 158 Jihohi Daban-Daban, A Tsarin Musayar Ɗalibai
Gwamnatin jihar Kano, ta kai rukunin farko na ɗaliban Makarantun Sakandire kimanin 158, zuwa jihohi biyar na ƙasar nan, a tsarin musayar Ɗalibai.
A ranar 19 ga watan Augustan da ya gabata ne dai, Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, ta gudanar da jarrabawa, domin tantance Ɗaliban da ke tsakanin shekaru 10 zuwa 13, da ke son shiga makarantun haɗaka, a jihohin Arewacin ƙasar nan guda 19, da Kwalejin Bilingual, da ke Yamai, a ƙasar Nijar.
Wani jawabi da Daraktan wayar da kan al’umma na Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, Balarabe Kiru ya fitar, ya bayyana cewar kashin farko na ɗaliban an kai su ne zuwa jihohin, Katsina, Borno, Benue, Jigawa, da ma Kebbi, a jiya (Lahadi).
A cewar jawabin kuma, ana tsammanin rukuni na biyu na ɗaliban da ke cikin wannan shiri za su tashi zuwa sauran jihohin Arewacin Najeriya, a ranar Laraba, 20 ga watan Satumban da mu ke ciki.
Ya kuma ƙara da bayyana, yadda Gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ke bada dukkannin goyon bayan da ake buƙata wajen samun nasarar shirin.