Labarai

Gwamnatin Kano Ta Maka Shugaban ARTV A Kotu

Gwamnatin jihar Kano, ta gurfanar da Daraktan gudanarwar gidan Talabijin na Abubakar Rimi, Mustapha Adamu Indabawa, tare da wani ma’aikacin tashar, Ibrahim M. Bello, gaban Kotu, bisa jerin tuhume-tuhume guda bakwai, waɗanda su ka shafi karkatar da dukiya ta miliyoyin Nairori.

Ƙunshin ƙarar ya ce laifukan mutanen biyu, sun ci karo da sashe na 211 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa gyaran fuska), tare da sashe na 121 (1), 123 (1) (a),126 (b) da 377 na dokar manyan laifuka ta jihar Kano (2019).

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar ce kuma ta shigar da ƙarar, bisa jagorancin Atoni Janar na jihar.

Hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano, ta gabatar da bincike kan lamarin, bayan ƙorafin da aka shigarwa da Gwamnatin Kano, kan Daraktan gudanarwar.

Bayan zurfafa bincike ne kuma sai hukumar ta rashawa ta gano badaƙala mai tarin yawa a talabijin ɗin, wanda hakan ne ya sanyata maka shi a Kotu, bayan gabatarwa da Gwamna rahoton.

Guda daga cikin cajin dai, ya zargi Indabawa da sauya akalar Naira Miliyan Tara, Da Dubu Ɗari Biyar da aka sanya a asusun gidan Talabijin ɗin, zuwa asusunsa na ƙashin kai, Daga Asusun FCMB mai lamba: 4968083012 na Talabijin ɗin, zuwa asusunsa na Eco Bank, mai lamba: 331 172332.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button