Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar Ziyartar Ɗaliban Makarantun Kwana
Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, ta sanya ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a matsayin ranar da Iyayen da Ƴaƴansu ke karatu a makarantun Firamare da Sakandiren jihar, na kwana (Boarding), za su kai musu ziyara.
Bayanin hakan, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, mai ɗauke da sa hannun Daraktan wayar da kan Jama’a na Ma’aikatar.
Sanarwar ta ƙara da bayyana cewar, Iyaye za su iya ziyartar ƴaƴan nasu a ranar ta Asabar ne, tun daga ƙarfe 9:00 na safiya, har zuwa 5:00 na yammacin ranar.
Ma’aikatar ta kuma yi kira ga Iyaye da su kiyaye dokoki da tsare-tsaren da aka tanada, a lokacin ziyarar.
Da ya ke nuna jin daɗinsa kan haɗin kai da goyon bayan da Ma’aikatar ta ke samu daga Iyayen yara da sauran al’umma, Kwamishinan Ilimi na Kano, Umar Haruna Doguwa, yabawa Iyayen ya yi, tare da yi musu fatan gudanar da ziyarar cikin ƙoshin lafiya, ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba.