Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Dawowa Da Kwalejin Shari’a Ta Aminu Kano Filayenta Da Aka Cefanar
Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta yi alƙawarin dawowa da Kwalejin Shari’a ta Aminu Kano filayenta, da ake zargin gwamnatin da ta gabata da cefanarwa.
Hakan na ɗauke ne, ta cikin wani jawabi da Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na jihar, Dr. Yusuf Ibrahim Ƙofarmata ya fitar, a ranar Talata, 14 ga watan Mayun 2024.
Inda Kwamishinan ya ce, sun ziyarci filayen da aka cefanar ɗin, a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.
Ya kuma ce, tuni gwamnatin Kano, ta bada umarnin tsayar da gine-ginen da ake gudanarwa a cikin filayen, ya na mai cewa, filayen na makaranta ne, kuma za su cigaba da kasancewa a ƙarƙashin makarantar.
Ga dai, abin da ya wallafa, a jawabin nasa mai taken: “FILAYEN LEGAL DA AKA CEFANAR A GWAMNATIN BAYA, ZASU DAWO MALLAKIN MAKARANTAR”.
Inda ya ce, “Jiya Litinin 13 Mayu, 2024 mun ziyarci filayen da gwamnatin baya ta cefanar, mallakin kolejin koyar da ilimin addini dana sharia, wato Legal.
“Mun tabbatar wa da hukumar wannan makaranta cewa gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf bazata lamunci cigaba da gine-gine a faɗin makarantun jihar Kano ba, kuma gwamnati ta bada umarnin dainawa nan take.
“Wannan filayen na makaranta ne, kuma zasu cigaba da kasancewa a ƙarƙashin wannan makaranta.
“Zamuyi ayyukan raya wannan makaranta da wannan filayen da yardar Allah.”, a cewar jawabin.