Ilimi

Gwamnatin Kano Za Ta Ɓullo Da Shirin ‘Ku Dawo Da Kujerunku’

Gwamnatin jihar Kano, ta bayyana shirinta na kaddamar da taron shekara-shekara kan makomar Ilimin jihar, bisa manufar ganin an farfado da fannin mai matukar tasiri ga rayuwar al’umma.

Membobin Kwamitin wannan taro sun kunshi: Daukacin masu ruwa da tsaki na fannin Ilimin jihar wadanda su ka kammala wa’adin ayyukansu na gwamnati, inda aikinsu zai shafi tallafawa gwamnati ta fuskar shawarwai kan yadda za a shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye fannin na Ilimi. Kwamishinan Ilimi na jiha, Umar Haruna Doguwa, shi ne ya bayyana hakan ya yin taron tattaunawar ma’aikatar da Manyan Ma’aikatanta, da ya gudana a babban dakin taronta.

Doguwa, ya kuma bayyana wannan yunkuri a matsayin wani mataki da gwamnatin ta yanzu ke dauka, wajen sake bunkasa tsarin Ilimi, ta hanyar aikin hadin guiwa.

Kwamishinan ya kuma kara da albishirin cewar, ma’aikatar za ta kaddamar da tsarin tattara rahotannin sassa, inda zaa dinga kara bibiyar aikin kowanne fanni bayan watanni uku-uku, dan tabbatar da gudanar da ayyukan da su ka dace.

Ka zalika, ya ce Gwamnati za ta bijiro da wani shiri mai taken ‘Ku Dawo Da Kujerunku’, inda Gwamnati za ta yi aiki da tsofaffin Daliban Makarantu wajen tabbatar da cewa kowanne tsohon dalibi ya bada tallafinsa na akalla kujera guda, ga makarantar da ta raine shi.

Kwamishinan, ya kuma jaddada kudurin gwamnatin, Abba Kabir Yusuf na bunkasa fannin Ilimin jihar Kano, dan ganin ya kere na sauran jihohin kasar nan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button