Gwamnatin Kano Za Ta Gina Gidaje A Kafafen Yaɗa Labarai Mallakinta
Gwamnatin jihar Kano, ta bayyana cewar, za ta gina gidaje, a kafafen yaɗa labaranta, domin amfanin ma’aikatan Kafafen da ke gudanar da Aikin dare.
Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da Daraktan Ayyuka na musamman, a Ma’aikatar yaɗa labarai, Sani Abba Yola, ya rabawa Manema Labarai, ranar Asabar, a birnin Kano.
Inda Yolan ya ce, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana hakan ne, a ya yin da ya karɓi baƙuncin membobin ƙungiyar Ma’aikatan Kafafen Yaɗa Labarai na Rediyo da Talabijin na ƙasa (RATTAWU), waɗanda su ka kai masa ziyara, a Ofishinsa.
Dantiye ya ce, tuni shirye-shirye su ka yi nisa wajen gina gidaje, a kafafen yaɗa labarai mallakin Gwamnatin Kano, domin sauƙaƙawa Ma’aikatan da ke gudanar da Aikin dare, wajen samun wuraren da za su zauna, a daren.
Ya kuma ƙara da cewar, hakan zai kasance wata mafita, kan ƙalubalen da Ma’aikatan da ke gudanar da Aiki da daddare, ko da sassafe su ke fuskanta, na barin gidajensu, zuwa wurin Aiki.
Kwamishinan, wanda ya yaba wa gudunmawar ƙungiyar ta RATTAWU wajen yaɗa sahihan Labarai a Jihar, ya tabbatar musu da samun goyon bayan ma’aikatarsa, wajen ganin sun gudanar da aikinsu, yadda ya dace, kuma cikin Kwanciyar hankali.
A jawabinsa tun da fari, Shugaban ƙungiyar ta RATTAWU reshen Jihar Kano, Babangida Mahmuda Biyamusu, ya ce sun je Ofishin Kwamishinan ne, domin taya shi murnar naɗin da ya samu, daga maigirma Gwamna.
Biyamusu, wanda ya jaddada cewar, ƙungiyar na da membobi sama da 3,000 a Jihar Kano, ya buƙaci goyon bayan Gwamnatin Kano, wajen shawo kan wasu daga cikin ƙalubalen da ƙungiyar ta ke fuskanta, da su ka haɗarda : rashin Ofishin Matsugunni, da rashin Abin Hawan gudanar da ayyukanta.
Inda kuma, ya ƙarƙare jawabinsa, da bawa Kwamishinan tabbacin samun goyon bayan ƙungiyar, wajen kwarmata ayyukan Gwamnatin ta Kano.